Posts

Showing posts from July, 2017

'Muryar Buhari ta ba ni tsoro'

Wasu masu sharhi a Najeriya suna fargabar cewa rashin lafiyar Shugaban Kasar Muhammadu Buhari ta tabarbare bayan da ya aike da sakon saukin muryarsa. Shugaban ya aike da saƙon bikin ƙaramar sallah ne ga 'yan Najeriya ranar Asabar. Lokacin ne karon farko da aka ji duriyarsa bayan ya kwashe kwana 49 yana jinya a Birtaniya. Hakan ya sa jama'a sun rika bayyana ra'ayoyinsu a kafofin sada zumunta a kasar, inda wasu suke cewa "muryarsa tana nuna cewa rashin lafiyarsa ya yi tsanani." Yayin da wasu ke cewa muryarsa ba ta sauya ba daga yadda suka santa ranar da zai tafi jinya Landan. Malam Kabiru Danladi Lawanti na Fannin Koyar da Aikin Jarida na Jami'ar Ahamdu Bello ta Zariya, ya ce halin rashin lafiyar "shugaban ya yi tsanani." "Duk wanda ya san Shugaba Buhari kuma ya saurari muryar da aka sanya ranar Asabar to wajibi ne ya tsorata." "Za ka ji muryar tana shakewa kamar wanda ya kamu da mura." in ji Lawanti. Ya ci gaba da ce...